A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, wakilan "Lajanar Harisanci" (Kwamitin Tsaro na Harkar Musulunci) sun gana da Sheikh Ibraheem Zakzaky, Jagoran Harkar Musulunci, a Abuja, babban birnin kasar Najeriya. Wannan zama an gudanar da shi ne domin murnar zagayowar watan Sha'aban da haihuwar Imamul Asr (A.F).
A yayin ganawar, Sheikh Ibraheem Zakzaky ya yi ishara da matsayin soja ga Imam Mahdi (A.F), inda ya bayyana muhimmancin kasancewa cikin shiri domin yin hidima. Ya ce: "Shi’a shi ne wanda kullum yake hidima ga Hazrat Waliyyul Asr (A.F) kuma yake bin hanya da tafarkinsa; domin a lokacin bayyanarsa, wadanda za su iya yin hidima a tare da shi su ne wadanda suka riga suka shirya kansu kuma suka kasance cikin shiri domin wannan ranar."
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, yayin bayanin adadin mataimakan Imam da matsayinsu, ya ce: "Bisa ga ruwayoyi, lokacin da Imam Mahdi (A.F) ya bayyana, yana da mabiya a matakai daban-daban; akwai 313 a sahu na farko, sai mutane 700 a mataki na gaba, haka nan sauran kungiyoyi suke biye. Abu mai ban mamaki shi ne cewa an bayyana cewa a cikin wadannan 313 (mafi kusanci), akwai mata da yawa. Wadannan abubuwa suna nuna cewa kafin bayyanarsa, dole ne mutum ya kasance cikin shiri domin yin hidima da zama soja ga wannan Janar."
Sheikh Zakzaky ya bayyana shiri kafin bayyanar Imam a matsayin daya daga cikin muhimman ma'anonin jiran bayyanarsa (Intizar), kuma ya kira wannan a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan mabiya (Shi'a). Daga nan sai ya tabo ayyukan Kwamitin Harisanci inda ya kara da cewa: "Daga cikin ayyukan rukunin Harisawa akwai gadi, tsaro, da gudanar da wasu ayyuka na musamman. Mafi mahimmanci shi ne cewa duk abin da muke yi, dole ne mu sanya Allah a gabanmu, kuma mu sauke nauyin da aka dora mana yadda ya kamata. Dangane da haka, za mu iya yin ishara da taimakon al'umma da ayyukan jinkai don neman yardar Allah."
Sheikh Zakzaky ya bayyana samun ikhlasi a cikin aiki a matsayin daya daga cikin sharuddan karbar ayyuka, sannan ya jaddada muhimmancin hakuri da juriya akan matsaloli da musibu, da kuma hadin kai a cikin ayyuka da shirye-shirye. Ya ce: "Duk wadannan suna nuna cewa idan aiki ya kasance saboda Allah, koda kuwa akwai maganganun soki-burutsu daga makiya ko abokai, to tunda aikin na Allah ne, zai haifar da sakamako mai kyau. Wannan shi ne babban burin da ya kamata mu sa a gaba."
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya kuma yi ishara da al'adar faretin Harisawa da ake yi a shekarun baya, inda ya ce: "A halin yanzu yanayi (na tsaro da siyasa) bai bayar da damar yin hakan ba, amma nan ba da dadewa ba za a yi shi. Shi ya sa aka gayyato kwamandojin shiyyoyi daban-daban domin mu tattauna wadannan batutuwa. Game da hakan, an gudanar da zama domin inganta ayyukanmu."




Your Comment